No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani magidanci mai suna Umar Ayuba ɗan shekara 37 ya rasu a wata rijiya da ke Kawon Maigari a ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kano lamarin.

Malam Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

“Mun samu ƙiran gaggawa da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, daga wani Mamuda Abdallah yace wani mutum ya maƙale a cikin rijiya.

“Nan da nan muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 5:32 na yamma,” in ji shi.

Abdullahi ya ci gaba da cewa, an nemi Mista Ayuba da ya taimaka wajen ɗauko zannuwan wasu mata da suka faɗa cikin rijiya.

KU KUMA KARANTA: Wata budurwa ta faɗi, ta mutu a cikin rijiya a Kwara

A cewarsa, wanda abin ya shafa, sai numfashinsa ya shaƙe a ciki saboda ƙarancin iskar.

“An fito da shi daga rijiyar a sume aka miƙa shi ga Isfekta Adamu Sani na rundunar ‘yan sandan Hotoro,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Ya ce an kai mutumin zuwa Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed amma bayan isowarsa wurin wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...