No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani matashi ɗan shekara 28 mai suna Misbahu Salisu, ya kashe yarinyarsa mai kwana ɗaya da haihuwa, saboda yafi son ɗa namiji.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mutumin da ke zaune a Doka Baici a ƙaramar hukumar Tofa a ranar Juma’a.

Hukumar ta sanar da kama shi ne a cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan rundunar Operation Mujahid Aminudeen ya fitar a Kano.

Mista Aminudeen ya ce wanda ake zargin ya sanar da jami’an hukumar cewa ya bai wa jaririyar wani maganin kashe ƙwari, mai suna Otapiapia.

“Salisu ya kuma saka wa mahaifiyar jaririn mai suna Sa’ade, ƙwaya a kofin shayi mai ɗauke da maganin barci kafin ya aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 17 ya kashe kansa a Bauchi

“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fi son ɗa namiji amma matarsa ​​ta haifi mace, wanda hakan ya sa ya kashe jaririyar,” in ji jami’in a cikin sanarwar.

Ya ce an miƙa wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...