Ya kashe mijin ƙanwarsa bisa zarginsa da bin mata

3
309

Wani mutum mai suna Iduh Hausa ya harbe sirikinsa har lahira, wato mijin ƙanwarsa, bisa zarginsa da cin amana tare da bibiyar matan banza, lamarin da ya abku a garin Umunede da ke ƙaramar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas a jihar Delta.

Lamarin wanda ya jefa al’ummar yankin cikin alhini, wata majiya ta ce ana tada jijiyoyin wuya a tsakanin al’umma dangane da abkuwwar lamarin.

“Mista Iduh Hausa ya harbe surukin nasa har lahira saboda kawai yana zarginsa da yin soyayya da wata mace, ya ce surukin nasa yana yaudarar ‘yar uwar sa.”

KU KUMA KARANTA:A gabana ‘yan sanda suka kashe makiyaya, bayan Abba Kyari ya nemi in ɗorawa Saraki laifin fashi – Ɗan fashi ga Kotu

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce: “Eh, ya tabbata; ba mu kama wanda ake zargi ba; har yanzu yana nan. Ana ci gaba da kokarin kama shi a duk inda ya ke ɓoye.” inji shi.

3 COMMENTS

Leave a Reply