No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 41, Tolulope Olowu da laifin daɓa wa wani Pablo mai shekaru 33 wuƙa, ya mutu har Lahira a kan ya ajiye mota a kan titinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya afkuwar lamarin a ranar Lahadi. Mista Hundeyin, Sufeto na ‘yan sanda, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:00 na dare a First Unity Estate, unguwar Badore a Ajah.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga bakwai, sun kama biyu a Zamfara

Ya ce an kai ƙarar lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Langbasa ranar Lahadi da misalin ƙarfe 2:00 na safe.

Kakakin ya ce wanda ake zargin da marigayin mazauna titin Gbadamosi ne a cikin gidan. “Sun samu rashin fahimtar juna game da ajiye mota a kan titi.

“A cikin haka, ana zargin Tolulope ya daɓa wa Pablo wuƙa a ciki kuma ya mutu nan take. “Bisa rahoton, tawagogin jami’an bincike daga sashin sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma suka ɗauki hoton.

“An ɗauke gawar kuma an ajiye ta a IDH Morgue, Yaba domin a tantance gawar,” in ji shi.

Mista Hundeyin ya ce an kama wanda ake zargin tare da nuna aikata laifuka, yayin da ake ci gaba da bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...