Hamas na ƙira ga Falasɗinawa a Isra’ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da su tashi tsaye don nuna adawa da mamayar Isra’ila a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke gabatowa.
Mai magana da yawun ƙungiyar Hamas, Osama Hamdan, da yake zantawa da manema labarai a birnin Beirut, ya ce Falasɗinawa su sanya kowane lokaci na watan Azumin ya zamo wata arangama.
KU KUMA KARANTA: Hana Falasɗinawa shiga Masallacin Ƙudus a watan Ramadan na iya haifar da tashin hankali – ‘Yan sandan Isra’ila
Ƙasashen Amurka da Qatar da Masar dai sun kwashe makonni suna ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza da kuma shawo kan ƙungiyar masu fafutukar ganin an sako wasu adadi mai yawa na mutanen da ake garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.