Ya kamata a fara jefe masu luwaɗi – Evariste Ndayishimiye

0
146

Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, ya bayar da shawarar cewa ya kamata a fara jefe masu aikata laifin auren jinsi a gaban taron jama’a

Evariste Ndayishimiye, ya kuma caccaki ƙasashen Yammacin duniya, kan yadda suke matsawa ƙasashen da ke kyamar auren jinsi lamba.

Tun a shekarar 2009 aka kafa dokar yanke zaman shekaru biyu a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin aikata luwaɗi ko kuma auren jinsi a Burundi, ƙasar da ta kasance mai tsatssauran ra’ayin addinin kirista a gabashin Afirka.

Ndayishimiye, wanda ya kasance mabiyin ɗarikar Katolika, ya ce auren jinsi haramun ne a addinin kiristancci kuma abin kyama ga al’adun ƙasar.

“Ni dai a ganina, idan muka samu irin waɗannan mutane da aikata auren jinsi ko kuma luwaɗi, to kuwa babu abin da ya kamace su, shine a samu babban filin taro a ajiye su, tare da ƙiran taron jama’a domin jefe su,” in ji Ndayishimiye.

KU KUMA KARANTA: An kama matashi kan zargin luwaɗi da ɗan shekara 4 a Gombe

Ya kuma yi tir da yadda ƙasashen Yamma ke matsawa ƙananan ƙasashe ala tilas sai sun halasta auren jinsi ko kuma a ddaina basu taimakon jin kai.

Ya ce, ‘yan Burundi da ke rayuwa a ƙasashen waje, waɗanda suka rungumi akidar auren jinsi su ci gaba da zama a can, ba sai sun koma ƙasar ba.

Auren jinsi dai haramun ne a ƙasashen gabashin Afirka dda dama, waɗanda ke da tarihin nuna kyama ga masu aikata hakan, da kuma nuna musu kyama, musamman waɗanda suka rungumi koyarwar addinin musulunci ko kuma kiristanci.

A watan Mayu ne, ƙasar Uganda, ta ayyana hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da aikata auren jinsi, abin da ya fuskanci suka daga ƙasashen yammaci da ƙungiyoyinsu.

Hakan ta sanya a wancan lokaci, Amurka ta ce za ta cire ƙasar Uganda daga cikin ƙasashen da take hulɗar kasuwanci da ssu, tare da haramta bayar da bisa shiga ƙasar ga manyan jami’anta, inda bankin bayar da lamuni na duniya, IMF ya dakatar da sabon Shirin bayar da bashi ga ƙasar.

A watan Maris ɗin wannan shekarar ne, Burundi ta yanke wa mutum 24 hukuncin zaman gidan yari, bayan samunsu da laifin auren jinsi.

Leave a Reply