Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashi na ƙasa na buƙatar bita don nuna haƙiƙanin gaskiya, yana mai jaddada cewa inganta rayuwar ‘yan Najeriya shi ne babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Shugaban wanda ya karɓi baƙuncin membobin ƙungiyar gwamnonin Progressive Forum (PGF) ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Hope Uzodinma na jihar Imo a fadar gwamnati, ya ce gwamnatocin ƙasa da na ƙananan hukumomi za su yi aiki kan mafi ƙarancin albashi, wanda tuni ya buƙaci “neman rai”

A cewar sanarwar da daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnatin jihar, Mista Abiodun Oladunjoye, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙara yin aiki kan wasu manufofin tattalin arziƙi da suka shafi jama’a.

“Muna buƙatar yin wasu ƙididdiga da binciken mai amfani akan mafi ƙarancin albashi. Dole ne mu kalli wannan tare, da kuɗaɗen shiga.

KU KUMA KARANTA: Za mu yi amfani da tsofi da sababbin takardun kuɗi a Najeriya – Tinubu

Dole ne mu ƙarfafa tushe da kuma amfani da kuɗaɗen shigarmu,” inji shi. Tinubu ya buƙaci Gwamnonin da su yi amfani da damar da aka basu na zaɓar su a cikin miliyoyin ‘yan ƙasa a Jihohinsu domin kawo sauyi a rayuwar al’umma, inda ya ƙara da cewa zai yi aiki don amfanin ‘yan Najeriya.

“Wannan taron ba baƙon abu bane a gare ni, kuma abubuwan da taron ya ƙunsa yana da matuƙar amfani.

Abokan hulɗa yana da ban sha’awa sosai. Wannan ya shafi aikin Najeriya ne ba Bola Tinubu ba,’’ inji shi.

Shugaban ya ce za a daidaita yawan kuɗaɗen musaya, yana mai cewa tsarin mulki na ci gaba.

“Na gaji kadarori da kuma bashin wanda ya gabace ni. Wannan shi ne karon farko da kuka shiga zauren majalisar, kuma wannan ne karo na farko da zan yi taro.

“A matsayinku na masu ci gaba kuma masu tunani a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kuna da rawar da za ku taka wajen wayar da kan jama’armu da kuma tabbatar da cewa mun gudanar da kanmu,” in ji Shugaban ya shaida wa Gwamnonin.


Comments

3 responses to “Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *