Ya je karɓo ‘ya’yansa a wajen tsohuwar matarsa, ‘yan’uwanta sun kashe shi da duka

0
353

Wani ɗan kasuwa mai suna Mallam Umar Tasiu, ya sha bulala, wadda ta yi sanadiyyar mutuwarsa har lahira da wasu surukansa suka yi masa a garin Minna na jihar Neja.

Wani maƙwabcinsa ya shaida wa Daily trust cewa, marigayin wanda ya kammala karatunsa a Jami’ar Al Azhar da ke Masar ya je ganin ‘ya’yansa da ke zaune da tsohuwar matarsa a gidan mahaifinta.

“Ya je ya ga ‘ya’yansa guda biyu da suke zaune tare da tsohuwar matarsa a gidan mahaifinta.  Sun rabu amma yaran suna wurin mahaifiyarsu. Ya je ya gansu amma surukansa na baya ba su so ya zo gidansu. 

Bayan isarsa sun ɗaure shi suka yi masa bulala har ya mutu a gidansu. An dawo da gawarsa gidansa a daren ranar Asabar kuma mun binne shi a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe,” inji majiyar.

KU KUMA KARANTA: An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mamacin ya rasu ne bayan an kai shi Asibitin ƙwararru na IBB da ke Minna, sakamakon raunukan da wasu ‘yan daba suka yi masa da bulala a gidan surukansa.

“A ranar 22/10/2023 da misalin ƙarfe 08:00, an samu rahoton ƙorafi kan aikata laifin kisan kai a sashin GRA;  cewa a ranar 21/10/2023 da misalin ƙarfe 23:00 wasu ‘yan daba suka kai wa wani Umar Tasiu ɗan Angwan Daji hari a Minna kuma ya samu munanan raunuka. 

An garzaya da shi Asibitin IBB da ke Minna, inda ya rasu. Ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kama waɗanda ake zargin,” in ji PPRO.

Wani abokin marigayin, Ahmad Sallah, a wani saƙon da ya wallafa a Facebook ya ce tsoffin surukai sun ƙi amincewa da auren ɗiyarsu da Umar saboda bambancin aƙidar addini.

“An yi wa Malam Umar duka har lahira a gidan surukinsa.  Alaramma mallam Umar tasi’u ɗan marigayi Alh Tasiu mai yadi.  Alaramma ɗan kasuwa ne, Hafiz, muhaddith, ya yi aure bayan ya kammala digirinsa a Jami’ar Al Azhar Egypt,” ya rubuta.

“Da alama ya fuskanci wani mawuyacin hali da tsohon surikinsa, wanda a ƙarshe ya yi sanadiyyar mutuwarsa, Alaramma Mallam Umar mutum ne mai kishin ƙasa, ɗan kasuwa ne, Hafiz, kuma muhadisi, ya kammala digirinsa a Jami’ar Al Azhar da ke Masar kafin ya yi aure.

“Ya bayyana cewa dangin matarsa suna da bambancin akidar addini, mahaifinta ɗan Izala ne, shi kuma ɗan ɗarikah ne, duk da rashin amincewar mahaifinta, sun yi aure sun haifi ‘ya’ya uku tare.

“Abin takaicin shi ne, saboda matsalar kuɗi a kasuwancin Alaramma, mahaifin matarsa ya yanke shawarar raba su, ya kai ƙarar Alaramma a gaban kotu, yana zargin Alaramma da koyar da ‘yarsa aƙidar ɗariqah.

“Duk da haka, Alaramma ya samu nasarar kare kansa a gaban kotu ta hanyar amfani da iliminsa mai yawa, duk da cewa ya ci nasara, mahaifin matarsa ya ɗauke ta da ƙarfin tsiya daga wurinsa, watau gidan Alaramma, lamarin da ya sa ala dole suka rabu aure ya mutu.

“Bayan shekaru, mahaifin har yanzu ya kwashe yaran daga hannun Alaramma.  Abin takaici, a lokacin da ya je gidan surukinsa yake yunƙurin karɓo ’ya’yansa daga hannun tsohuwar Matarsa da surukinsa, sai suka ƙira shi ɓarawo, yanayi da ya sa aka kai masa hari da duka ya mutu har lahira.

Leave a Reply