Yaƙi tsakanin Isra’ila da Falasɗinu, Rasha da Ukraine ya shafi tallafin kuɗin kiwon lafiya a Afirka – UNICEF

0
197

Rikice-rikicen da ke faruwa a Gaza da Ukraine sun yi matukar shafar tallafin kuɗaɗe da ake samar wa harkokin kiwon lafiyar al’umma da kuma ƙananan yara a Yammaci da Tsakiyar Afirka, a cewar wani jam’in Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF.

Shugaban sashen kula da mata masu juna-biyu da jarirai da kuma lafiyar matasa na UNICEF a Yammaci da Tsakiyar Afirka Dr. Boon Alexandre ya ce kuɗaɗen da ake kashewa a fannin kiwon lafiya a yankunan sun ragu zuwa kusan kashi 50 cikin 100 sakamakon yake-yaken da ake yi.

“A duk lokacin da aka samu wani al’amari babba kamar rikicin Isra’ila da Falasɗinu da kuma yaƙin Rasha da Ukraine, hankulan manyan ƙasashen duniya kamar Amurka da Birtaniya da kuma China kan karkata zuwa ga wannan batun, “kamar yadda shugaban ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a Lome, babban birnin Togo a ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA: Hotunan Falasɗinawa mata da matasa da Hamas ta sa aka saki daga kurkukun Isra’ila

Ya yi wannan jawabi ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar kan matsalolin kiwon lafiyar jama’a da abinci mai gina jiki da kuma lafiyar yara a Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Dr. Alexander ya bayyana cewa a yanzu haka ƙasashen da ke bayar da agaji sun fi mayar da hankalinsu ne wajen tallafawa ayyukan jinkai a yankunan da ke fama da rikice-rikice da yake-yake.

Jami’in na UNICEF ya ce halin da ake ciki a yanzu na iya kawo tsaiko a tallafin da ƙasashen Afirka suke samu wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da mutuwar jarirai da sauran matsalolin kiwon lafiyar jama’a.

Ya bukaci gwamnatocin ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afrika kan su ƙara kasafin kuɗaɗen kiwon lafiyarsu domin cike gibin da ake samu a kuɗaɗen da ƙasashe masu ba da taimako suka haifar.

Taron kafafen yaɗa labarai da aka gudanar na kwanaki uku ya samun halartar ‘yan jaridu a ɓangaren kiwon lafiya kusan 60 daga ƙasashe 23 na yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.

Leave a Reply