Wutar lantarki ta lalata dukiya ta sama da naira miliyan 38 a Kwara

Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta bayyana yadda wata gobara da ta auku, sakamakon matsalar wutar lantarki ta ƙone wasu gidaje biyu a Ilorin, babban birnin jihar, a safiyar ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun ce wutar ta fara ne da misalin ƙarfe 12:31 na dare daga wani shagon sayar da Fenti da ke Balogun Afin a unguwar Ita-Kure a garin Ilorin. An ce an yi ƙiyasin asarar dukiya ta kimanin miliyan 38.9 sakamakon tashin wutar.

Hassan Adekunle, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce wani gini mai hawa ɗaya da wani gida da ke gefen shagon fentin sun ƙone ƙurmus.

KU KUMA KARANTA: Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa

A cewar Adekunle, musabbabin tashin gobarar ya faru ne sakamakon ƙarfin wutar lantarkin, inda ya ƙara da cewa sinadaran da ke cikin abubuwan da ke ƙonewa sun taimaka wajen tashin gobarar wadda ta lalata dukiya ta sama da Naira miliyan 38.8 yayin da aka ceto dukiya ta Naira miliyan 52.5.

“Baya ga wasu gine-gine biyu da gobarar ta lalata, wasu shaguna biyar da ke kusa da wurin da abin ya shafa. ‘Yan kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar tare da hana ta ci gaba da ruruwa zuwa gine-ginen da ke maƙwabtaka da su.

“Gobara ce mai girma kuma girman ɓarnar da ta yi ta haɗa da sinadaran abubuwan da ke ƙonewa,” in ji Adekunle.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *