Wutar lantarki ta kashe miji da matarsa da ‘ya’yansu biyu a jihar Taraba

0
162

Mutane huɗu daga cikin iyalin gidan mutane biyar a jihar Taraba sun mutu bayan da wutar lantarki ta kama su a unguwar Dinyavo da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba.

Mahaifi da mahaifiyarsa da yara biyu suna cikin gidansu lokacin da ibtila’in wutar lantarkin ta auku.

Mazauna yankin sun ce suna zargin cewa wutar lantarkin ta faru ne sakamakon ƙarfin wutar lantarki da aka samu daga na’urar sadar da wutan lantarki ta ƙasa ya haddasa lamarin.

‘’Da safiyar yau, sai ga wani fashewa daga na’urar taransifoma.  Kowa ya fita da gudu hayaƙi ya biyo baya.  Bayan ‘yan daƙiƙu, kowa ya fara ihu, kafin mu ankara sai ga wasu gidaje da yawa sun cika da hayaƙi.

Na yi iya ƙoƙarina na ceto su, duk abin ya ci tura, domin sun kulle kansu, amma da muka yi nasarar karya ƙofar, sai muka gane cewa wutar lantarki ta kama su, su ma maƙwabtan sun firgita, suka garzaya da su asibiti.” Inji wani ganau

An ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiyar gawarwaki.

Leave a Reply