WHO ta ce ta kasa tuntuɓar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, a safiyar Lahadi ya tabbatar da cewa babu wata hanya da ƙungiyarsa ta WHO za ta tuntuɓi asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza.

“WHO ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza, a daidai lokacin da ake samun rahotanni masu ban tsoro na ƙarin hare-hare,” kamar yadda Tedros ya bayyana a shafin X.

Mista Tedros ya bayyana cewa wasu rahotanni sun ce wasu da suka gudu daga asibitin an harbe su inda aka kashe su, wasu kuma an ji musu rauni.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *