Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, a safiyar Lahadi ya tabbatar da cewa babu wata hanya da ƙungiyarsa ta WHO za ta tuntuɓi asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza.
“WHO ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza, a daidai lokacin da ake samun rahotanni masu ban tsoro na ƙarin hare-hare,” kamar yadda Tedros ya bayyana a shafin X.
Mista Tedros ya bayyana cewa wasu rahotanni sun ce wasu da suka gudu daga asibitin an harbe su inda aka kashe su, wasu kuma an ji musu rauni.