Wata yarinya ‘yar shekara 14 ta kashe kanta

Wata yarinya ‘yar shekara 14 mai suna Desola Adeoye ta kashe kanta a unguwar Shogunle da ke ƙaramar hukumar Oshodi-Isolo a jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa Desola ta ɗauki maganin kashe ƙwari ne domin gujewa ci gaba da azabtarwa, bayan da ake zargin ta sha fama da rikicin cikin gida a hannun mahaifinta, Sunday Adeoye da kuma kishiyar mahaifiyarta.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Desola ta dawo daga darasinta na makarantar rani, sai kishiyar lmahaifiyarta ta fara yi mata barazana, inda ta shaida mata cewa idan mahaifinta ya dawo zai dake ta.

Desola, wadda ta damu da wannan barazana, rahotanni sun ce ta fice daga gidan ta sha maganin ƙwarin da aka ajiye a gidan.

KU KUMA KARANTA: Walƙiya da tsawa ta kashe sayar da shayi a jihar Kwara

Rahotanni sun ce an garzaya da ita wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa inda ta rasu.

Mahaifinta ya yi gaggawar ɗauko gawarta daga asibiti ya kaita gida da nufin binne ta a ɓoye.

Sai dai an ce jami’an ofishin ‘yan sanda na shiyyar Shogunle da maƙwabta suka sanar da su sun daƙile shirinsa.

Wata maƙwabciyarta, wacce ta ja hankalin wata ƙungiya mai zaman kanta, Advocates for Children and Vulnerable Persons Network (ACVPN), a kan lamarin ya shaida wa Vanguard cewa: “Marigayi Desola da kannenta biyu suna fuskantar cin zarafi a gida a kai a kai daga mahaifinsu, da kishiyar uwarsu a duk lokacin da suka yi kuskure.

“Desola ta kashe kanta saboda tsoron ka da mahaifinta ya yi mata dukan tsiya.

“Ƙungiyar Ci gaban Al’ummar Shogunle a Oshodi (CDA), a lokuta da dama, sun gargaɗi mahaifinsu da kishiyar mahaifiyarsu da su daina cin zarafin da ake yiwa ‘ya’yansu musamman, marigayi Desola Adeoye,” in ji maƙwabciyar.

Babban jami’in gudanarwa na ACVPN, Mista Ebenezer Omejalile, yayin da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, ya yi ƙira ga gwamnatin jihar Legas, da ‘yan sandan Najeriya da kuma ƙungiyar lauyoyin Najeriya da su ceto sauran yaran biyu da har yanzu suke hannun ma’auratan tare da samun adalci ga yaran da Desola.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *