Wata ‘yar sanda ta roƙi kotu ta raba aurenta, saboda yawan duka daga mijin

Wata ‘yar sanda mai suna Angela Adams a ranar Talata ta roƙi wata kotun gargajiya da ke zamanta a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, da ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta, Titus, kan rikicin cikin gida.

Matar ta faɗi haka ne a cikin ƙarar da ta shigar a gaban kotun game da mijinta.

“Mijina yakan yi min duka a duk lokacin da muka samu ‘yar rashin fahimta. Yakan yi min duka kamar ƙaramar yarinya.

“Koda yaushe idona ya ke nema idan yana duka na. Ko rannan ma da ya yi min duka, sai da ya kawo min naushi a fuskata, na yi sa’a na kare da hannuna amma duk da haka sai da naushin ya ji min rauni a hannu na,” in ji ta, lokacin da ta ke kuka.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta raba auren wata 10 ta hanyar “Khul’i”

Ta ce mijin nata ya karɓi rancen kuɗi naira dubu 750,000 da sunan ta a wani banki.

“Lokacin da na tambaye shi me zai yi da kuɗin, sai ya gaya min cewa ya sayi katako ne da kwanon rufi ɗaki da kuɗin, amma daga baya na ji cewa ashe wani gida ya kama haya ya gyara shi ya saka wata mace a ciki.”

Yaudara ta ya yi na aure shi, ban san ma ashe ya na da ‘ya’ya biyu ba, kuma kwanan nan ya yi wa wata ciki.”

“Ina roƙon wannan kotu mai daraja da ta ba ni riƙon ɗan ɗaya tilo na wannan aure tare da raba auren kafin mijina ya kashe ni kuma ba za a samu wanda zai kula da yaro na ba”.

Wanda ake ƙara,Titus wanda shi ma ɗan sanda ne, bai halarci zaman kotun ba.

Sai dai mai shari’a Thelma Baba, ta bayar da umarnin a kai ƙarar wanda ake ƙara ta hannun lauyansa, sannan ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, domin jin ta bakin wanda ake ƙara da kuma kare kansa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *