Wata uku gwamnatin da na gada ba ta biya albashi ba a Zamfara – Gwamna Dauda

1
396

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ce yana tafiyar da jihar ne a kan bashi tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya kuma ce gwamnati ta ka sa biyan albashin ma’aikata da alawus-alawus, ciki har da hukumomin tsaro a jihar.

Gwamna Lawal, wanda ya bayyana haka a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Litinin, ya ce gwamnatin da ta shuɗe ta bar ƙa sa da naira miliyan huɗu ne kawai kacal a asusun jihar.

A cewarsa, manyan ɗaliban makarantun jihar ba su rubuta jarabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma, (WAEC), da hukumar jarrabawar NECO ba, saboda rashin kuɗi.

KU KUMA KARANTA: Ban mallaki kadarorin naira tiriliyan 9 ba – Gwamnan Zamfara

“Na kasance ina tafiyar da al’amuran jihar a kan bashi tun lokacin da na hau kujerar gwamnan Zamfara.

Na samu asusun baitul malin jihar ba kuɗi. Na ga asusu ɗaya da kusan Naira miliyan 3 zuwa 4 a ciki,” inji shi.

“Kusan watanni uku ke nan, kuma har yanzu ba mu biya albashin ma’aikata ba.

Idan aka dubi dukkan hukumomin gwamnati, wutar lantarkin da ake amfani da su a gine-ginen ya katse saboda basussukan da ake bi na miliyoyin daloli.

“Hukumomin tsaro, watanni uku kenan ba a biya su alawus ɗin da ake ba su na ayyukan yau da kullum ba.

Yanzu haka ɗaliban manyan makarantun sakandire ba su rubuta jarabawar WAEC da NECO ba saboda gwamnati na bin sama da naira biliyan ɗaya.”

Yayin da yake watsi da iƙirarin da tsohon gwamnan ya yi na cewa ya bar wa sabon gwamnan Naira biliyan 20, gwamna Lawal ya ƙalubalanci shi da ya gabatar da shaidun da ke nuna adadin kuɗin a bainar jama’a.

Ya ce, “Lokacin da na ji haka, sai na ce su zo su nuna mini asusun, su bayyana shi tare da shaidar asusun da aka ajiye irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe,” inji shi.

“Idan ina da wannan adadin kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ke iƙirarin sun bar jihar, zan biya dukkan ma’aikata albashin su, in kuma samar da isassun kuɗaɗen ga jami’an tsaro domin kare jihar.

“Batun ruwa, kusan watanni huɗu kenan babu ruwa a Gusau.

Dole ne in yi aro don siyan sinadarai na ruwan. “Na kuma roƙi wasu Indiyawan da suka baiwa jihar wasu injunan samar da ruwa.

Idan jihar za ta sayi waɗannan injunan, za ta kashe sama da Naira miliyan 200.

“Ba zan iya cewa na magance matsalar ruwa ta Zamfara ta dindindin ba, amma zan yi iya ƙoƙarina don ganin an magance matsalar,” in ji Dauda.

Gwamnan ya ce zai tabbatar da an biya ma’aikatan jihar albashinsu kafin gudanar da bukukuwan Sallah. “Ina so in tabbatar wa ma’aikatan gwamnati a Zamfara cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu don ganin an biya dukkan albashin ma’aikata kafin Sallah,” in ji shi.

“Zan yi duk abin da ya kamata don biyan albashin ma’aikata. Ina yin duk abin da ya dace don nemo tallafi don biyan albashin da ake binsa.

“Ya danganta da adadin lamunin da zan iya samu. Idan har abin da jihar za ta iya biya shi ne albashin wata ɗaya, zan yi iya ƙoƙarina wajen biya shi domin haƙƙinmu ne mu tabbatar mun gudanar da aikin da ya rataya a wuyanmu na biyan ma’aikata abin da suka yi aiki a kai.”

1 COMMENT

Leave a Reply