Wata mata ta zane Alƙali da bulala

0
329

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Abakaliki, jihar Ebonyi, ta tisa ƙeyar wata mata mai shayarwa ‘yar shekara 32, Misis Ann Akpa bisa zargin cin zarafin wani Alkali.

‘Yan sanda sun gurfanar da Akpan Ann a gaban ƙuliya bisa zarginta da yi wa majistare Lilian Igwesi bulala da sanda a ranar 28 ga watan Agusta 2023 a lamba 32 Hill Top Road, Abakaliki.

Wanda ake tuhuma a cikin ƙarar tuhuma biyu mai lamba MAB / 630c/2023 an kuma zarge ta da haddasa rashin zaman lafiya ta hanyar zuba datti a cikin gidan Majistare.

KU KUMA KARANTA: Mijina yayi wa ubana dukan kawo wuƙa, ya ɓata mini sana’a

Mai gabatar da ƙara na ‘yan sanda, ASP Chinagorom Eze, ta ce ta aikata laifukan da za a hukunta su a ƙarƙashin sashe na 335 da 249 (d) na kundin laifuffuka, Cap.  33, Juzu’i na 1, Dokokin Jihar Ebonyi, Nijeriya, 2009.

Wanda ake tuhumar ta ƙi amsa laifuka biyun da ake tuhumarta da su na cin zarafi da haifar da rashin zaman lafiya.

Lauyan wanda aka yi ƙara A. J. Uguru, Esq,  ya nemi a ba shi belin wanda ake ƙara, inda ya bayyana cewa laifin da ake tuhumata da su laifuka ne wanda ake iya bayar da beli.

Sai dai Alƙalin kotun, Lynda Ogodo ta ƙi bayar da belin, ta kuma bayar da umarnin tsare ta a gidan yari na Abakaliki, sannan ta ɗage zaman Kotun zuwa ranar 27 ga watan Satumban 2023.

Leave a Reply