A wani yanayi mai matuƙar ɗaure kai, wata mata mai matsakatan shekaru mai suna Nkechi Blessing Nwobodo, ta yi kashin wasu fasassun kwalabe a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Nkechi, kamar yadda wakilinmu ya samu labari na zaune ne a garin Ifo da ke jihar Ogun.
A cewar matar, a zantawarta da Aminiya ranar Juma’a, “Na biyo tawagar ’yan uwana mata a motar haya daga Igun zuwa Legas da kuma sauran wasu jihohin kasar nan za mu tafi ziyarar Ibada wani ƙauye da ake ƙira Biakpan yankin ƙaramar hukumar Biase da ke jihar Kuros Riba.
“Akwai wani rafi mai ruwan mu’ujiz da ruwansa yake wucewa ta gefen wurin ibadar da muka je sauƙe farali na tsarin addinin mu na Kiristanci bangaren Olumba.”
KU KUMA KARANTA: Thomas Fuller, mai ƙwaƙwalwar lissafi ta ban al’ajabi
Ta ci gaba da cewa, “Mun yi imani ruwan yana warkar da cutuka ko wanne irin mutum yake fama da shi da mu mabiya muka yi imani da hakan.
“Mu mabiya ɗarikar Brotherhood wato ta Olumba Olumba Obu. Sai ɗaukacinmu muka shiga cikin ruwan rafin muna yin kurme saboda mu samu waraka daga cututtukan da suke damun mu a jikinmu a wannan ƙauye.
“Dama kuma ina fama da yawan laulayi da ciwon jiki sai na yanke shawarar bari in ɗebi ruwan na sha na yi wanka da shi ko na samu lafiya.
“Bayan mun gama aikin ziyarar ibadar mun koma gida kwanaki kaɗan sai na riƙa jin ciwon mara da ciwon baya kafin mu baro Biakpan zuwa gida Kalaba.
“Tun Kafin ma mu gama abin da muke yi na ziyarar ibadar a Kalaba na mayar da ruwan nan da na ɗebo.
“Daga Nan fa sai na fara jin wasu abubuwa na motsi a cikina kamar su fito, na ji na matsu, sai na yi wuf na tafi banɗaki naje na tsuguna. Ina tsugunen ne na riƙa jin motsin wasu abubuwa a dubura ta na sanya hannu in jawo su.
“Nan fa na tsorata saboda yadda na riƙa jawo abubuwan suna faɗowa ne har suka gama fita ban damu ba sai na Sanya waya ta ta hannu na ɗauki hoton abin da na kasayar sai na ga ashe wasu ɓalli-ɓallin fasassun kwalabe ne na kasayar,” in ji Nkechi.