Wata mata ta mutu a rijiya, a lokacin da ta take ɗiban ruwa a Kwara

1
419

Wata mata mai suna Misis Jamiu Sikirat mai shekaru 57 da haihuwa ta mutu bayan ta faɗa rijiya a lokacin da take ɗiban ruwa a Ilọrin babban birnin jihar Kwara.

Mummunan lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin ranar Litinin.

Marigayiyar wacca mazauniyar gidan na Ile-Agunko ne a yankin Adeta a ƙaramar hukumar Ilorin ta yamma, an bayyana cewa ta zame ta faɗa cikin rijiya.

Sai dai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kwara sun tsince ta a mace.

KU KUMA KARANTA : Mutane huɗu sun mutu, da dama sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Ibadan

Da yake magana kan lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Hassan Hakeem Adekunle, ya ce an miƙa gawar ga wani ɗan uwa mai suna Alfa Abdulganiyu Akuko.

“Jami’an kashe gobarar mu sun amsa ƙiran gaggawar, kuma sun samu nasarar ciro gawar marigayiyar daga rijiyar.

Ya ƙara da cewa “Matar ta je ɗiban ruwa a rijiyar ne a lokacin da ƙafarta ɗaya ta zame ta faɗa cikin rijiyar.”

Adekunle ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan lamarin, inda ya ƙara da cewa daraktan hukumar, Yarima Falade John Olumuyiwa, ya buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan a harkokinsu na yau da kullum.

“Ya kuma yi ƙira da a hana jama’a tura yara ƙanana su ɗebo ruwa a rijiyoyi.”

1 COMMENT

Leave a Reply