No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata mace mai juna biyu ta haihu bayan naƙuda ta zo mata ba zato ba tsammani a cikin jirgin KLM da ke kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam daga Legas.

Lamarin dai ya tilasta wa jirgin yin saukar gaggawa a ƙasar Sifaniya.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne cikin daren Litinin, inda ɗaya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin KLM mai lamba 588, ƙirar Boeing 777, ta fara naƙuda.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kai matar wadda ba a bayyana sunanta ba gaban jirgin, inda ta haifi ‘ya mace.

KU KUMA KARANTA: Yadda matan wani mutum su huɗu suka haihu a rana guda a sansanin ‘yan gudun hijira

Bayan nan ne sai jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Barcelona inda ma’aikatan lafiyan da aka ƙira suke tsaye suna jira.

An ce uwa da ‘yar duka suna cikin ƙoshin lafiya.

Mai magana da yawun kamfanin sufurin jiragen sama na KLM, Marjan Rozemeijer, a ranar Talata ta ce, “Zan iya tabbatar da cewa an haifi jaririyar a cikin jirgin KLM mai lamba KL 588 da ke kan hanyar zuwa Amsterdam a ƙasar Netherlands daga Legas.

Saboda dalilai na tsare sirrin mutum ba zan iya yin wani ƙarin bayani game da haihuwar ba.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...