Wata bazawara a Kano, tana tura ruwa a baro, tana sayarwa domin ta ciyar da ‘ya’yanta marayu

0
191

Wata mata ‘yar Najeriya mai matsakaicin shekaru, Gambo Haruna, wacce mijinta ya rasu shekaru shida da suka gabata bayan ya sha fama da jinya, ta kwashe shekaru biyu tana tura baro, tana sayar da ruwan da za ta kula da ‘ya’yanta shida, kamar yadda jaridar Daily Tryst ta ruwaito.

Tana zaune a gidan haya a wani tsohon gidan laka, tana zaune a ɗaki ɗaya, wanda take biyan Naira 12,000 duk shekara a Gadar Katako, yankin Rimin Keɓe a ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano.

KU KUMA KARANTA: Abincin da ake nomawa a arewacin Najeriya, ya isa a ciyar da mutanen ƙasar nan – Farfesa Abdulkarim

Rayuwa ta yi matuƙar wahala ga wannan mata ‘yar fiye da shekaru 30.  Kuma ta rungumi duk wani ƙalubalen da ta fuskanta a rayuwa.

Gambo ta ce ta yi aiki dare da rana domin ta kula da ‘ya’yanta saboda ba za ta so yin bara ko yin wani abu da ya saɓawa shari’a ba.

Sai dai ta ce halin da take ciki ikon Allah ne, kuma ta yi addu’a don ganin Allah ya kawo mata ɗauki cikin wannan yanayi.

Dangane da harkar sayar da ruwa da kuma ƙalubalen da take fuskanta, Gambo ta ce tana buƙatar ƙarin kuzari, inda ta ce a kullum tana samun kuɗi tsakanin Naira 750 zuwa 1,000, inda daga nan ta riƙa biyan Naira 150 ga mai baro da ta karɓi haya.

Leave a Reply