No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wata matar aure ‘yar shekara 18 mai suna Khadija Adamu da laifin lakaɗa wa ‘yar kishiyarta mai shekara 5 duka ta mutu har lahira a yankin Kandahar da ke jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, 2023, yayin wata ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Bauchi.

CP Muhammed ya ce an kama Khadija ne bayan da wani Abdulaziz Adamu ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa wadda ake zargin ta lakaɗa wa Hafsat Garba dukan tsiya, sakamakon haka ta samu munanan raunuka kuma likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBUTH) ya tabbatar da rasuwarta.

A cewar Kwamishinan, wanda ake zargin ta amsa laifinta ba tare da gardama ba.

Ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da ita a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...