No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ana zargin wata ɗalibar aji huɗu a Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOU) da ke Jihar Ogun ta kashe kanta ta hanyar shan guba a wani ɗakin otel.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce an gano ɗalibar, Adaze Doris Jaja, mai shekaru 31 ne a sume a cikin ɗakin, kumfa na fitowa daga bakinta, da kwalbar maganin kashe kwari a gefenta.

Odutola ta shaida wa ’yan jarida a Abeokuta ranar Talata cewa ranar 27 ga watan Janairu da karfe 7:30 na safe, an kai rahoton lamarin ga jami’in ’yan sanda na Ago-Iwoye, yankin da abin ya faru.

Odutola ta “Daraktan otal din Be-Happy da ke Ago-Iwoye, Oduniyi Adelaja, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda cewa da misalin karfe 6 na safiyar ranar, ya samu labari daga wani ma’aikacin otal ɗin cewa an iske Adaeze a sume a ɗakinta kumfa na fitowa daga bakinta, da wata kwalbar maganin kashe ƙwari a gefenta.

KU KUMA KARANTA: Wata yarinya ‘yar shekara 14 ta kashe kanta

“Nan take aka garzaya da ita asibiti inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarta,” in ji jami’ar.

Odutola ta ce an ziyarci inda lamarin ya faru kuma an gano fankon robar maganin kashe ƙwarin.

Ta kuma bayyana cewa an kai gawar ɗalibar zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na OOU domin bincike.

Jami’ar ta ƙara da cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kuma ta sanar da hukumomin jami’ar game da lamarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...