Wasu ‘yan uwa 2 a Zariya sun binne ƙaninsu da ransa

0
95
Wasu 'yan uwa 2 a Zariya sun binne ƙaninsu da ransa

Wasu ‘yan uwa 2 a Zariya sun binne ƙaninsu da ransa

Daga Idris Umar, Zariya

An sami rahoto cewa wasu ‘yan uwa biyu sun binne ƙaramin ƙaninsu ɗan shekara 16 da ransa mai suna Abubakar sakamakon ɓatan waya a garin Zariya na jihar Kaduna.

Sai dai ‘yan sanda sun yi nasarar kama waɗanda suka aikata laifin da suka hadar da ɗaya mai shekaru 22 da kuma 18, bayan da wani mutum ya hangi kan Abubakar yana reto a rami cikin wani kango.

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan’uwan sun samu rashin jituwa dalilin wata waya da ta bata a Abuja, inda suke aiki.

Wani bayani ya nuna cewa ‘yan uwan sun biyo Abubakar har Zariya inda suka binne shi da ransa a matsayin azabtarwa.

Kwamishiniyar ma’aikatar jin dadin jama’a da ci gaban jama’a ta jihar Kaduna, Rabi Salisu ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba.

“Sai da suka daure yaron, kuma suka kulle bakinsa kana suka binne shi a cikin rami inda suka bar kansa kawai a waje a wani kango.

Ban taba ganin an binne wani da rai ba sai a cikin fim. Yaron mai suna Abubakar ɗan shekara 16 ‘yan uwansa sun binne shi ne saboda bacewar wayar, kamar yadda Punch ta rahoto.

“Sun tona rami, inda suka daure hannayensa bayan sunrufe bakinsa. Sannan suka binne shi, kansa kawai suka bari a waje a lulluɓe da tsumma a cikin wani kango kusa da wata gona.

Wani bawan Allah ne da ya ji yaron yana tari wanda hakan ya jawo hankali wasu manoma har suka ceto yaron, kamar yadda faifan bidiyon da ya yaɗu a shafukan sada zumunta ya nuna.

“Waɗanda suka aikata laifin masu shekara 22 da ɗan uwansa, ɗan shekara 18 ne ƴan sanda sun yi nasarar kama su, za mu je kotu bayan bincikensu.
Gwamnati ba za ta ɗauki hakan da wasa ba, wajen kare hakkin yara da sauran wadanda ake tauye hakkinsu a jihar Kaduna,” inji Rabi Salisu

KU KUMA KARANTA:Kama sojan da ya harbe matashi a Zariya abun yabawa ne – Atiku

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya ce wadanda ake zargin suna tsare kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Hassan ya ce masu laifin sun amsa laifin su.
A halin da ake ciki kuma, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da ci gaban jama’a ta jihar, ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa ta dauki kwakkwaran mataki bayan afkuwar lamarin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wanda aka binne, Abubakar Aliyu, ya tsallake rijiya da baya, kuma tuni aka kuɓutar da shi. ‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargin.

“Jami’in jin daɗin jama’a da ke Zariya ya ziyarci yankin da lamarin ya afku domin duba halin da ake ciki tare da bayar da tallafin da ya dace. Ma’aikatar ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci kuma za su ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin.

“Kuma Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kakkausar murya tare da jaddada ƙudirinta na kare hakki da walwalar ƴan kasa musamman ƙananan yara.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here