Wasu Sarakuna da Hakimai sun yi murabus daga muƙaman su
Sarakuna da Hakimai aƙalla goma sha uku ne suka yi murabus daga muƙaman su a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato, yankin da ya jima yana fama da matsalolin rashin tsaro.
Duk da yake ba’a cika samun irin wannan lamari ba a Najeriya, Sarkunan da hakimai sun bayyana dalilan su na ɗaukar wannan matakin.
‘Yan Najeriya sun daɗe suna fama da matsalar rashin tsaro, halin ƙunci, fatara da rashin samun ci gaba a wasu wurare, kuma duka suna taka muhimmiyar rawa wajen wasu matakai da ‘yan ƙasar ke ɗauka ga rayukan su.
Wasu daga cikin iyayen al’umman da suka yi murabus ɗin, sun haɗa da Uban doman Gobir, Katukan Gobir, Mai garin Taka-tsaba, da sauransu, sun bayyana dalilan su na daukar matakin ne saboda koma baya da yankin ke fuskanta, da matsalar rashin tsaro, kuma sun karkata wilayar su zuwa ga sanata mai wakiltar su Ibrahim Lamido saboda a cewar su yana da zimmar fitar da su daga kangin rayuwa da suke ciki.
KU KUMA KARANTA: Shugaban hukumar tattara bayanan sirri na ƙasa ya yi murabus
Ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masarautu da jihar Sakkwato ta ƙi cewa komai akan lamarin, amma shugaban ƙaramar hukumar Sabon birni, Ayuba Hashimu yace, wasu daga cikin mutanen da suka ce sun ajiye sarautun su, sun dawo daga baya sun warware wannan magana kuma sun aminta da tsarin shugabanci da suke a kai tun farko.