Wasu mazauna Kano sun bayyana damuwarsu kan ƙarin farashin data na MTN

0
14
Wasu mazauna Kano sun bayyana damuwarsu kan ƙarin farashin data na MTN

Wasu mazauna Kano sun bayyana damuwarsu kan ƙarin farashin data na MTN

Daga Jamilu Lawan Yakasai

A cikin tsare-tsaren wata-wata, yanzu ana sayar da 1.8GB akan N1,500, wanda a baya ake sayar da 1.5GB akan N1,000. Haka nan, 15GB yanzu yana N6,500 maimakon N4,500, sai kuma 20GB da aka ƙara zuwa N7,500, daga N5,500.

Bayan haka, an kara farashin aika saƙon rubutun karta kwana (SMS) zuwa N6.00, wanda ke nuna karin 50%. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da karin farashin kiran waya ba.

KU KUMA KARANTA:Kamfanonin sadarwa na MTN, Glo da Airtel za su ƙara kuɗin data

A halin yanzu, sauran kamfanonin sadarwa kamar Airtel, Glo, da 9mobile ba su aiwatar da wannan ƙarin farashi ba.

Hukumar NCC dai ta amince da karin farashin da kaso 50%, duk da cewa kamfanonin sadarwa sun nemi karin 100% saboda hauhawar farashin gudanar da aiki.

Hukumar ta ce ta yanke wannan shawara ne bayan tuntubar masana da kwararru daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.

“Muna fahimtar wahalhalun da al’ummar Najeriya ke fuskanta, amma wadannan matakai za su taimaka wajen tabbatar da ci gaba da zuba jari a fannin sadarwa, wanda zai kawo ingantattun ayyuka da haɗin gwiwa mai kyau,” in ji NCC.

Hukumar ta kara da cewa karin farashin zai taimaka wajen samar da ingantaccen sabis, kyakkyawar kulawa ga abokan hulɗa, da kuma fadada wuraren da sadarwa ke aiki a fadin kasar.

Leave a Reply