Wasu makiyaya a Borno sun yanke hannuwan wani manomi a gonarsa

0
77
Wasu makiyaya a Borno sun yanke hannuwan wani manomi a gonarsa

Wasu makiyaya a Borno sun yanke hannuwan wani manomi a gonarsa

Wasu da ake kyautata zaton makiyaya ne sun yanke hannuwan wani manomi da suka shiga gonarsa da dabbobinsu a jihar Borno.

Shigar makiyayan da dabboninsu da kuma aika-aikan da suka yi wa manomin ya faru ne bayan arangama da mai gonar da misalin karfe 1.30 na ranar Juma’a.

Majiyar Zagazola Makama ta ce manomin ya yi yunkurin kore makiyayan daga gonarsa, amma suka yi turjiya, inda daya daga cikinsu ya far masa, ya sare masa hannawa biyu.

Sakamakon haka aka garzaya da manomin zuwa Asibitin Gubio, daga bisani aka wuce da shi Asibitin Maiduguri domin ci gaba da kula da lafiyarsa.

KU KUMA KARANTA: Ƙaramar Hukumar Kwami ta kafa kwamitin tsaro saboda rikicin manoma

Bayan afkuwar lamarin, al’ummar yankin sun kasance cikin zaman ɗar-ɗar, inda aka yi gargaɗin cewa jama’a su guji ƙauyen Bassam Galomari.

An kuma umarci hukumomin tsaro su ɗauki mataki da nufin shawo kan rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here