No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Ana zargin wata bazawara da jagorantar wasu mata 7, zuwa gidan wata matar Aure mai suna Maryam Mohd Sani a unguwar Chiranci karamar hukumar Kumbotso ta jihar kano da zuwa har gida suka lakada mata dukan kawo wuka.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa matan sun zo da Duwatsu, Tabarya da kuma Muciya tare da balle kofar gidan matar.

Bayan matan sun shiga cikin gidan ne suka rufeta da duka har sai da ta futa daga haiyacinta , tare da zuba mata Ruwan Fitsari Roba biyu a cikin ta, da kuma yunkurin jefa ta Rijiya.

Al’ummar Unguwar sun, ne mi taimakon jama’a domin kama matan da ake zargi da yanzu haka suka gudu.

KU KUMA KARANTA:Yayi wa tsohuwar budurwar shi dukan kawo wuƙa don ta ƙi auren shi

Mijin matar mai suna Muhammad Sani ya bayyana damuwarsa akan wannan al’amari harma ya zargi wata makociyarsu da gaiyato sauraran matan da suka yi wa matar sa dukan kawo wuka.

Sani ya kara da cewa a halin da ake ciki matar ta sa bata cikin haiyacinta da yanzu haka ta ke kance a Gadon Asibiti .

Wakilin mai unguwar Chiranci Gidan Kwari, Usman Ya’u ya bayyana cewa , yana cikin gida aka kirawo shi a waya da cewar matan suna fada .
“Nan danan nazo naga wadda aka yi wa duka”.acewar sa.

Wata shaidar gani da ido ta ce wata bazawara ce dake makotaka da gidan ta gaiyato matan domin huce haushi akan zargin ta da cewa yayanta bata hanyar Aure aka same su ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...