Wasu fitinannun ɓeraye sun tilasta wa manoma kwana a gona a Kano

0
132

Wasu murguza-murguzan ɓeraye sun tilasta wa manoma kwana a gonakin su domin yin gadi, sakamakon ɓarna da su ke yi musu ta amfanin gona a yankin ƙananan hukumomin Kura, Bunkure da Garin Mallam a jihar Kano.

Manoman dai sun bayyana cewa ɓerayen sun zame musu annoba, musamman ma ganin cewa duk irin maganin kashe bera da aka saka musu, amma sai su ƙi ci, lamarin da ya sanya su ka ɗauki matakin yin fito-na-fito da su.

Sun kuma baiyana cewa idan suka bar gona to sai dai a yiwa manomi jaje, inda su ka ce ɓerayen ba sa tsoron mage ballantana muzuru.

Mallam Ahmed sani kura wani malamin gona ne ya yankin Dan Galawa dake ƙaramar hukumar Kura daga ƙungiyar masu anfani da ruwan noman rani, ya yi ƙira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki.

Ya kuma yi ƙira ga masana da su bada gudummawar hanyar da za a samu nasarar kashe ɓerayen ta hanyar zuba musu guba a abinci.

KU KUMA KARANTA: Manoma sun koka kan yadda makiyaya ke cinye musu gonaki a Gombe

A nashi ɓangaren, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, shugaban ƙungiyar masu noman tumatur ta ƙasa reshan jihar Kano ya ce wannan ɓeraye sun daɗe suna uzzirawa manoma kuma suna zuwa ne lokacin sanyi.

Ya koka da cewa duk irin girman gonar manomi idan ba a yi wasa ba sai sun cinye ta.

“Wato wasu irin murguza-murguzan ɓeraye ne masu laifin basira domin duk irin maganin ɓera da ka saka musu a abinci banza su ci ba. Idan ka saka magani a abinci ka ajiye wani abincin maras magani, to maras maganin za su ci.

“Duk yawan shuka da aka yi sai sun cinye ta. Hakan ne ya sanya dole manoma da yawa su ka koma kwana a gonakin su domin gadin ganin gonar su da kuma kashe ɓerayen.

“Muna ƙira ga gwamnati da ta kawo mana ɗauki sannan muna ƙira ga masana ilimin dabbobi dan su tallafa mana da hanyoyi ko nau’in maganin da za a riƙa saka musu suna mutuwa,” in ji Yadakwari.

Leave a Reply