Wasiƙar Yakubu Gowon ta zo a ƙurarren lokaci – Masana

0
96

Ra’ayin masana ya bambanta dangane da wasiƙar da tsohon Shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowan ya rubuta wa shugabannin ECOWAS, yayin da waɗansu suke gani ba za ta yi tasiri ba ganin cewa ya zo a ƙurarren lokaci, wasu kuma na ganin za ta yi tasiri, la’akari da waɗanda abin ya shafa.

Jim kaɗan bayan da wasiƙar tsohon Shugaban Najeriya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin nahiyar Afrika wato ECOWAS, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya karaɗe ko’ina a kafafen yaɗa labarai, masana a fannin tsaro, diflomasiyyar ƙasa da ƙasa, masu fashin baƙin siyasa suka yi ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kan tasirin wasiƙar ko akasin haka.

A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi a kan siyasa da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa kuma Shugaban kamfanin kasuwanci da zuba jari GITC, Mal. Baba Yusuf, ya ce wasiƙar ta zo a makare saboda irin tsauraran matakan da ƙungiyar ta ɗauka tun farko.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da kashe ɗan-fashin dajin da ya addabi jihohin arewa

A wani ɓangare kuma, ƙwararre a fannin tsaro da diflomasiyar ƙasa da ƙasa, Kabir Adamu ya bayyana cewa, jaddada mahimmancin rayuwa da walwalar ɗan’adam da tsohon Shugaban ya yi a cikin wasiƙar sa zai iya taimaka wa sakon sa ya yi tasiri wajen ɗinke ɓaraka tsakanin Shugabannin ƙungiyar ta ECOWAS.

A nata bayanin, wata matashiya ‘yar Jamhuriyyar Nijar ta ce al’umar ƙasarta na maraba da saƙon na tsohon Shugaban Najeriya, tana mai cewa babu fatan da ‘yan Nijar ke da shi a halin yanzu kamar a buɗe musu iyakokin ƙasashen da ke maƙwabtaka da su gabanin tunkarowar watan Ramadan.

Tun bayan kafa ƙungiyar ECOWAS a matsayin babbar hukumar shiyya ta yammacin nahiyar Afirka a shekarar 1975, ficewar mambobi uku lokaci guda shi ne mafi girman kalubalen da ta fuskanta a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

Leave a Reply