Wani mutum ya gutsire mafitsara da leɓen wani yaro ya cinye (bidiyo)

0
284

Al’ummar dake zaune a kwanan Fara-kwai da ke kan titin Kaduna zuwa Zaria, jihar Kaduna, sun ga wani abin tashin hankali a lokacin da wani mutum ya kama wani yaro ɗan shekara 10, yana chizgar naman jikin wannan yaron yana cinyewa.

Mutumin ya gutsire wani ɓangare na mafitsarin wannan yaron da gefen leɓen sa, kuma ya cinye, kamar yadda kakar yaron ta bayyana mana.

“Ya shaƙe wuyan shi kuma, kafin jama’a suka kawo masa ɗauki”.

Bayan an ceto yaron ne, mai suna Abubakar Ibrahim, an garzaya da shi wani ƙaramin asibitin shan magani dake kamfanin Zango, dake kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Mun samu zantawa da yaron, duk da maganar shi bata fita, ya kuma bayyana mana yadda ya faɗa tarkon mutumin.

KU KUMA KARANTA: Abun sha’awa: Yaro mai fuskar al’ajabi da shuɗin launin idanu

Yace “an aike shi gidan wata mata, sai ita matar ta ƙara aikensa wani gidan ya karɓo mata kuɗi, ya tafi ya karɓo kenan, sai ya haɗu da mutumin a lungu, ya kama shi ya cire mishi igiyar wandon shi, ya kama mafitsarin shi, ya gutsure, ya kuma kama leɓen shi, ya cire ya cinye, ya fara ihu kenan, sai ya shaƙe wuyan shi, yace bari kawai ya kashe shi”.

Malamar jinyar asibitin, mai suna Hajiya Hadiza Bello, ta tabbatar da kawo musu yaron cikin mummunar yanayi.

Suka yi kokarin su na taimaka mishi, har ya ɗan dawo cikin yanayin shi. Suka ɗinke mafitsarin shi, har su ka tabbatar ya iya fitsari.

Kakar yaron ta buƙaci a bi ma yaron hakkinsa.

Mutanen garin sun kama mutum dan su kashe shi, kamar yadda Malam Yahaya Muhammad, kwamandan ƴan sa kai na KADIP, ya faɗa mana, sai de sun kwace shi, sun miƙa shi ga ‘yan sanda.

Ɗan uwan yaron, Abubakar Maharazu, yace yaron yana asibiti ana kula da shi, kuma yana samun sauki.

Ɗan masanin Fara-kwai, Nura Umar, yace wannan be taɓa faruwa ba a wannan garin ba. Ya kuma cewa, za su iya kokarin an kwato wa yaron hakkinsa.

Rahotanni sun ce, mutumin ya taho ne daga jihar Jigawa domin karɓar magani a garin na Fara-kwai. Nan gaba za a ji ta baƙin hukumomin ƴan sanda.

Ku kalli bidiyon a nan:

Leave a Reply