No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mutum ya ƙone tsohuwar budurwarsa a cikin barikin sojoji na Oyo

Rundunar ‘Yansandan Jihar Oyo ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruq, da ake zargi da ƙone tsohuwar budurwarsa bayan dangantakarsu ta lalace.

Jaridar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a wani barikin soja da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, wanda ya wallafa bayanai kan lamarin a shafin X , ya bayyana cewa wanda ake zargin ya ce shi da wadda abin ya shafa sun yi alkawarin cewa ba za su taɓa rabuwa ba.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Adamawa, sun kama saurayi da budurwa da su ka yi garkuwa da kansu

Sai dai, bayan soyayyarsu ta lalace, an ce Faruq ya fusata ƙwarai, inda daga bisani ya zuba wa budurwar mai sannan ya banka mata wuta.

Bayan faruwar lamarin, wasu sojoji da ke cikin barikin sun ceto matar tare da garzaya da ita asibiti, kafin daga bisani su kama wanda ake zargin.

Makama ya rubuta cewa: “Wadda abin ya faru da ita, Omolola Hassan, an ce an zuba mata mai sannan aka ƙone ta da wuta, bayan wanda ake zargin ya fusata kan yadda soyayyarsu ta zo karshe.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ta wayar tarho a ranar Alhamis, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Osifeso ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan al’amarin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...