No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mutum a Legas ya rasu sakamakon azumin kwana 19

Rundunar ’yan sandan jihar Legas, ta tabbatar da rasuwar wani mutum mai shekara 58, sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumin ba tare da ya sha ruwa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

Ya ce lamarin ya faru ne a yankin Alagbado na jihar a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na safe.

Ya ce ɗan uwan mamaci ne, ya kai rahoto faruwar lamarin ofishin ‘yan sanda na Alagbado a ranar Litinin cewa ɗan uwansa ya rasu sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumi.

KU KUMA KARANTA: Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu

Hundeyin ya ce, “Babu wani abu da aka zargi ya faru da shi, ‘yan uwansa sun buƙaci a kai gawar don birne ta.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...