Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa a Jigawa

0
174

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 32, Samuel Shegun bisa zargin kashe mahaifiyarsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, AT Abdullahi ya tabbatar da hakan, a yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, ‘yansanda sun gano gawar wata mata ‘yar shekara 47 mai suna Esther Adekanla wadda aka fi sani da Hadiza Nakowa a gidanta da ke garin Dutse.

Ya ce bayan binciken da aka gudanar, jami’an tsaro daga sashin binciken manyan laifuka na jihar Dutse, sun kama wani Samuel Shegun da ke daura da tashar jiragen ruwa ta Awajil Dutse, dangane da kisan gilla da aka yi wa mahaifiyarsa, mai suna Esther Adekanla da ke wannan adireshin tare da raunata ƙanwarsa.

KU KUMA KARANTA: Mahara sun kashe mutane 15 a wani Coci a Burkina Faso

An kama wanda ake zargin ne ta hanyar bin diddigin lambar wayar marigayiyar, wanda ake alaƙanta shi da aikata laifin.

Mahaifiyarsa

Ya ce “Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa, a ranar 12/02/2024 da misalin ƙarfe 22:00, mahaifiyarsa ta dawo daga inda take sayar da abinci, kuma ta fara faɗa da yarinyar, Christiana Michael har ta kai ga riƙe wuƙa. A ƙoƙarinsa na kuɓutar da yarinyar, sai ya ja ta baya a lokacin da suka faɗi gaba ɗaya, sai ta yanke wuyan ta da wuƙar da ta faɗa akai.

“Lokacin da ya fahimci girman laifin da aka aikata kuma baya son jami’an tsaro su ƙira shi, sai ya yanke shawarar ɗauke wayar ta, ya kulle gidan sannan ya yi nesa da unguwar.”

Kwamishina Abdullahi ya ce ƙaramar yarinyar da ke samun sauƙi daga raunuka daban-daban da ta samu, har yanzu tana ƙarƙashin kulawar likitoci da kuma karɓar magani.

Ya ce yarinyar ta tabbatar wa ‘yan sanda cewa wanda ake zargin shi ne ya aikata laifin kisan. Kenan batun cewa mahaifiyar tasa ta faɗi ne akan wuƙa ta yanke ba gaskiya ba ne, shi ne ya kashe ta da kansa.

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin gurfanar da shi gaban ƙuliya, ya girbi abin da ya shuka.

Leave a Reply