No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani matashi ya kashe mahaifinsa, ya binne shi a gidansu

Rundunar ’yan sandan jihar Neja, ta kama wani matashi mai shekara 29 mai suna Mizanmil Abubakar da laifin kashe mahaifinsa Abubakar Adawa mai shekara 65 a duniya.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Waisu Abiodun ne, ya bayyana hakan a Minna a ranar Talata, inda ya ce an kai rahoton faruwar lamarin sashen ‘yan sanda na Kpakungu.

Ya ce, “A ranar Talata da misalin ƙarfe 10 na safe ne aka samu labari a sashen Kpakungu cewa a ranar Litinin wani Abubakar Adawa ya ɓace a unguwar Barkin-Sale a Minna.

Abiodun ya ce jami’an ’yan sandan da ke aiki a sashen ƙarƙashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na yankin sun ziyarci gidan da wani Mizanmil Abubakar mai shekara 29 da kuma Aisha Abubakar, uwa da ɗanta ke ciki domin yi musu tambayoyi.

Ya ce, “An yi bincike sosai a gidan baki ɗaya, kuma abin mamaki, an gano gawar wanda ya ɓace a cikin wani rami mara zurfi a gidan.”

KU KUMA KARANTA: Mayaƙan ‘Boko Haram’ a Borno sun kashe ɗan sanda da ƙona motocin sintiri

Abiodun, ya ce matashin ya amsa laifin kashe mahaifinsa ne sakamakon ya tsane shi.

Kakakin ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi amfani da fartanya ne wajen kashe mahaifin nasa, sannan ya birne shi a wani rami.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kafin miƙa wanda ake zargin a kotu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...