No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani matashi ɗan shekara 19 ya daɓa wa budurwarsa wuka ya hallaka ta a kan kuɗi naira dubu biyar a Jihar Bauchi.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammad Wakil, ya bayyana cewa tuni ’yan sanda sun kama wanda ake zargin.

Wakil ya ce, “abin ya faru ne a lokacin da wanda aka kashen ta buƙaci a biya ta naira 5000 da take bin (wanda ake zargin) bashi, a kan harkokin da suka yi a baya.

“Ana cikin haka sai gardama mai zafi ta shiga tsakaninsu har ta kaiga ya daɓa mata wuƙa, ta samu mummunan rauni wanda ya kai ga mutuwarta.”

KU KUMA KARANTA: An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

Wakil ya bayyana cewa a ranar 18 ga watan Disamba, 2023 jami’an tsaro suka kama shi a unguwar Sabon Layi Kano Road Bauchi bisa zargin kashe Emmanuella Ande.

A cewarsa, an kama shi ne sakamakon ƙiran da wani mutum ya yi musu cewa wanda ake zargin ya shiga ɗakin otal da ke Bayan Gari, ya daɓa wa budurwarsa wuƙa a kirjinta.

“Jama’ar sun yi yunƙurin ceto ta, inda suka ɓalle kofar ɗakin, inda shi kuma ya daɓa wa wani Zaharaddeen Adamu wuƙa a hannun hagunsa,” in ji shi.

Wakil ya ce, ’yan sanda sun hanzarta kai ɗauki, inda suka ceto wanda ake zargin, aka kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi inda likita ya tabbatar da rasuwar ta, kuma aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa.

Hakazalika an kai Zaharadeen an yi masa magani a asibitin ’yan sanda, aka sallame shi, wanda ake zargin kuma a halin yanzu ana ci gaba da bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...