No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani ɗan kasuwa, Ssaalongo Nsikonenne Habib Ssezzigu, ya auri mata bakwai a rana guda a ƙasar Uganda.

An yi bikin auren ne a ƙauyen Bugereka, a gundumar Mukono  ranar Lahadi, 10 ga Satumba, 2023.

Biyu daga cikin mata bakwai da ya aura ’yan’uwan juna ne.

An fara gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 8 na safe, inda aka kai Amaren ɗakin gyaran jiki domin yin salon gashi, kafin a sanya su a cikin motocin dakon kaya na Super Custom, ɗauke da faranti na musamman wanda ke ɗauke da sunayen kowace Amarya.

KU KUMA KARANTA: Mutumin da ya auri kada, ya ce zai riƙe ta cikin aminci babu cutarwa

Bayan sun yi musabaha na aure, Nsikonnene da matansa guda bakwai sun gudanar da gagarumin jerin gwano ƙarɓashin jagorancin masu tuƙa keke babura da ake ƙira “boda”, suka bi ta garuruwan Kalagi, Kasana, da Nakifuma, kafin su isa gidansu da ƙarfe shida na yamma.

An fara bikin ɗaurin auren ne da kaɗe-kaɗe a yayin da ma’auratan ke tafiya a cikin ayarin motoci, yayin da jama’a suka yi ɗafifi a bakin titi domin shaida bikin.

Wasu mutane sun ka sa gaskata cewa gaskiya ne wannan abu yana faruwa, wasu sun ce wannan shi ne karo na farko da za su halarci irin wannan taron ɗaurin aure.

Matan sun haɗa da Mariam, Madina, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, da Musanyusa, wacce ita ce matar Habib ta farko kuma tana tare da shi tsawon shekaru bakwai.

Haka Habib ya sayo sabbin motocin a matsayin kyauta ga kowane daga cikin matansa.

A wajen liyafar, an shirya kujerun angonta, kowane da sunayensu.

Nsikonnene a jawabinsa a wajen liyafar, ya yabawa matansa bisa yadda suke yi masa biyayya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...