An tsinci gawar wani ɗan kasuwa mai shekaru 35 a duniya da ake zargin ya rataye kansa a wani ɗaki da ke unguwar Sharaɗa a Kano.
An gano gawar matashin ɗan kasuwar ce da wasikar da ya rubuta cewa: “A yi hakuri. Amma sauran ba sai na bayyana ba.”
Aminiya ta samu labarin cewa marigayin yana zaune ne a ɓangaren samari a gidan da lamarin ya faru shi da ɗan uwansa.
Ɗan uwan nasa mai suna Hamisu ya shaida mana cewa, “Na dawo daga sallar asuba, matata na shirin dafa wa ’ya’yanmu abinci, tana neman ashana domin ta kunna wuta amma babu.
“Sai ta tuna yakan yi amfani da ashana wajen kunna turaren wuta.
KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar mai gadi rataye a wata makarantar firamare a Gombe
“Da ta aiki yaronmu ya karɓo ashana a wajensa, sai yaron ya gan shi a rataye, sai ya koma da gudu yana ihu wai wani ne ya rataye yaya. Sai na garzaya ɗaki na ga gaskiya ne”.
Da aka tambaye shi ko yana da wata matsala da marigayin, sai ya ce, “Ba mu samu wata matsala ba. Abin da na sani shi ne a kwanakin nan yana cikin damuwa, kuma a matsayinmu na ’yan kasuwa, mukan ji haka idan kasuwa ta yi saɓanin yadda muke so.
“Mu ’yan kasuwa ne kuma muna sana’ar sayar da kayan ɗaki, amma shi wani lokaci yana saye da sayar da tsofaffin kayan.
“Na lura da alamun damuwa a tare da shi a kwanakin nan saboda ya karɓi kuɗi a hannun wani ya sayo kayan da kuɗinsu ya kai N400,000 a Rijiyar Zaki daga hannun wasu mutane suka kai shi gidan da suka ajiye kayan suka ce ya dawo wata rana ya kai su.
“Da ya nemi lambar wayarsu, sai suka ce tun da ya ga gidan zai iya dawowa kowane lokaci, amma da ya koma bai samu gidan ba.
“Abin da ya jawo masa damuwa ke nan domin kuɗin ba nasa ba ne kuma mai kuɗin ya matsa masa a kan ya biya shi,” in ji ɗan uwan nasa.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani bayani kan lamarin daga rundunar ’yan sandan jihar kan faruwar lamarin.