Wani matashi a Kano ya kai wa ‘yan sanda kuɗin da ya tsinta
Daga Idris Umar, Zariya
Wani direba mai shekaru 36, mai suna Safiyanu Mohammed ya miƙawa ‘yan sandan jihar Kano wata jaka ɗauke da maƙudan kuɗaɗe da ya tsinta.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kano, SP Abdallahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sa direban wanda mazaunin unguwar Rangaza kwatas ne a ƙaramar hukumar Ungogo, ya tsinci jakar ne a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta, 2024 a hanyar Hadejia kusa da mahaɗar Dakata.
KU KUMA KARANTA: An karrama ɗan agajin da ya tsinci miliyan 100
A maimakon ya tafi da kuɗin, Mohammed ya zaɓi ya mika wa hukumar ƴansanda jakar da domin gano mai jakar don bashi abarsa.
Rundunar ‘yan sandar jihar ta Kano ta yi ƙira ga jama’a da su taimaka musu da cikakkun bayanai da zai sa a gano mai jakar don bashi jakarsa.