No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mai shayi a Jigawa ya kashe saurayi saboda taliyar yara

Wani mai sana’ar sayar da shayi ya lakaɗa wa wani saurayi duka har sai da rai ya yi halinsa saboda taliyar yara a Jihar Jigawa.

Wannan mummuan lamari ya faru ne bayan mai shayin ɗan shekaru 40 ya zargi saurayin mai shekaru 20 da sace masa kayan shayi, a garin Jigawar Tsada da ke Karamar Hukumar Dutse.

Mai shayin ya zargi mamacin da satar taliyar yara da burodi da madara da kuma man fetur a shagon, lamarin da ya kai ga sa-in-sa a tsakaninsu.

Ana cikin haka ne mai shayin, a fusace ya ɗaure saurayin da igiya, ya yi masa bulala har ya kai ga daina mostsinsa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansandan Jamus na neman wani mutum da ya kashe mutane uku da wuƙa

Daga bisani ’yan sanda suka je suka ƙwace shi suka garzaya zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, amma da zuwansu aka tabbatar da mutuwarsa.

Sanarwar faruwar lamarin da kakakin rundunar ’yan sanda da Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya sanyawa hannu a ranar Talata ta ce, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin, inda ya bayyana cewa yawan satar da mamacin ke masa ne ta fusata shi.

A cewasa, wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa a baya ya sanar da iyayen mamacin, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

Jimi’in ya ce, makwabta sun ce sun ji kukan mamcin na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da ’yan sanda suka iso.

Daga nan sai ya ce bayan  cikakken bincike za a gurfanar da wanda ake zargi da kisan a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...