Wani mai maganin gargajiya ya raunata kansa yayin gwajin maganin bindiga

0
46
Wani mai maganin gargajiya ya raunata kansa yayin gwajin maganin bindiga

Wani mai maganin gargajiya ya raunata kansa yayin gwajin maganin bindiga

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya samu raunin harbin bindiga yayin da yake gwada laya mai kare harbi a unguwar Kuchibiyi, ƙaramar hukumar Bwari, a birnin Tarayya, Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi, Samson Ayuba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da mutumin, a ƙoƙarinsa na gwada tasirin layarsa mai kare harbi, ya harbi kansa a ciki.

Ya bayyana cewa mai maganin ya yanke jiki ya faɗi nan take, sannan wasu maƙwabta suka yi gaggawar daukar sa zuwa asibiti.

“Mutumin bokane, yana haɗa magunguna da layoyi na gargajiya. A ranar Alhamis, ya yi ƙoƙarin gwada bindiga a kan kansa bayan ya sanya laya mai kare harbi, amma layan ya kasa kare shi,” in ji shi.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan FCT, SP Adeh Josephine, ta ce wanda abin ya faru da shi ya yi amfani da bindigar gargajiya ya harbi kansa a ciki.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Katsina sun ceto fasinjoji 14 daga hannun ‘yan bindiga

Ta ce jami’an ‘yansanda daga sashen Byazhin sun yi gaggawar kai ɗauki inda suka tarar da wanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali.

Ta ce bayan kai shi asibiti, ƴansanda sun bincika ɗakin mutumin inda su ka samu bindiga ƙirar gida da kuma layoyi daguraye.

Leave a Reply