Wani magidanci ya kashe kansa kan zargin matarsa da bin maza

0
90
Wani magidanci ya kashe kansa kan zargin matarsa da bin maza

Wani magidanci ya kashe kansa kan zargin matarsa da bin maza

Wani magidanci mai ’ya’ya uku ya rataye kansa bisa zargin matarsa da bin maza a yankin Masaƙa da ke Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Kakakin ’yan sandan jihar,  DSP Nansel Ramhan, ya shaida mana a ranar Laraba cewa a safiyar Litinin aka tsinci gawar mutumin a rataye a cikin aji a Makarantar Crystal da ke Masaƙa.

Ya ce wani malamin makarantar ne ya kawo rahoto cewa an ga wani baƙon mutum an rataye ta a jikin silin ɗin ajin.

“Bayan samun rahoton ne DPO da jami’ansa suka je suka kai shi Babban Asibitin Mararaba, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu, aka ajiye gawar a mutuware,” in ji DSP Ramhan.

Ya ce babu wata takarda ko saƙo da mamacin ya bari, amma rundunar tana bincike don gano musabbabin mutuwar.

KU KUMA KARANTA: An ɗaure ‘yan Najeriya 2 bayan damfarar wani ɗan Amurka da ya kashe kansa

Game da zargin cin amanar auren da matar mutumin ke yi ne ya sa shi kashe kansa, jami’in ya ce ba shi da masaniya, amma suna bincike.

Amma wani sako da wakilinmu ya yi karo da shi a Facebook ya yi iƙirarin cewa magidancin ya  hallaka kansa ne bayan da ya gano cewa abokansa suna kwana da matarsa suna ba ta kuɗi.

Saƙon ya yi iƙirarin cewa ko da mutumin ya tunkari matar, sai ta shaida masa cewa tana lalata da su ne saboda shi ya kasa ɗaukar ɗawainiyar ciyar da iyalisa.

A cewar sakon, matar ta shaida wa mijin nata mai shekaru 38 cewa da kuɗin da ake biyan ta take ciyar da kanta da shi da ’ya’yansu uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here