Aƙalla ‘yan bindiga biyu ne aka aika da su barzahu, yayin da suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da iyalan wani magidanci a yankin Jalingo, Jihar Taraba.
Lamarin ya faru cikin daren ranar Asabar, yayin da magidanci ya yi tirjiyar hanawa a tafi da iyalin sa, a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya ce an kashe ‘yan bindiga biyu yayin da ‘yan sanda suka je ceton waɗanda aka yi garkuwa da su, bayan an yi masu ƙiran gaggawa.
Sai dai kuma majiya a Unguwar Baraya inda lamarin ya faru, ta shaida wa wakilin mu cewa maigidan ne mai suna Arɗo Yahaya ya kashe gogarman ɗan bindiga ɗaya da kan sa, inda ya yi kukan-kura ya rarume shi, ya riƙa caccaka masa wuƙa, yayin da aka yi ƙoƙarin kama shi.
KU KUMA KARANTA: Sojojin saman Najeriya sun kashe kwamandojin ISWAP uku a Borno
Wani mazaunin unguwar mai suna Mustapha Ja’afaru, ya ce ‘yan bindigar sun fasa ƙofar gidan Yahaya wajen ƙarfe 1 na dare.
Ya ce a lokacin da wasu suka haura ta katanga, sai Yahaya wanda dama ya laɓe da zundumemeyar wuƙar sa, ya auka wa ‘yan bindigar.
“Ko da ya ji motsin su, sai ya samu wuri ya laɓe, sannan ya yi sararaf ya rarumi gogarman su, ya riƙa caccaka masa wuƙa, ya kashe shi nan take.
“Daga nan sai ya yi kururuwa. Amma kafin a kawo ɗauki, har ‘yan bindiga sun kama ‘ya’yan sa ƙanana biyu, bayan sun raunata Yahaya.”
Sai dai kuma cikin ikon Allah, ‘yan sanda sun bi su, kuma sun ceto yaran.
Ya ce washegari an ga gawar wani ɗan bindiga a cikin daji, wanda ya faɗi ya mutu yayin ƙoƙarin gudu bayan an ji masa ciwo.