Wani magidanci ya ƙudiri aniyar yin tattaki da keken hawa, daga Damaturu zuwa Kano don taya Gwamna Abba murnar nasara a kotun ƙoli

0
106

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Wani magidanci mai suna Usman Mohammed ɗan kimanin  shekaru 49 ɗan asalin jihar Kano da ke zaune a Damaturu babban birnin jihar Yobe ya ƙudiri aniyar yin tattaki na kwanaki 4 daga Damaturu zuwa Kano a kan keken hawa  domin murnar nasarar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun  ƙoli ta ƙasa a makon da ya wuce.

Malam Usman Mohammed mazaunin Damaturu wanda ya kwashe sama da shekaru 35 a Damaturu ya ce ya kammala dukkan shirye-shiryen fara wannan tattaki nasa.

A cewarsa, dalilan da suka sa zai yi  wannan yi tattakin ta amfani da  keken hawa zuwa Kano shi ne don ya je ya taya murna ga  gwamnan jihar Kano da al’ummar Kano bisa nasarar da gwamna Abba Yusuf ya samu a kotun ƙoli ta ƙasa dangane da taƙaddamar da aka riƙa yi kan wannan Zaɓe nasa.

“A cewar sa Abba Gida-Gida mutum ne mai kirki wanda a kodayaushe  matsalar mutanensa ne a gaban sa fiye da komai wadda da na Isa ina fatan saduwa da shi don isar da saƙon magoya bayan sa a nan Damaturu  na taya shi murna.

KU KUMA KARANTA: Saƙon Gwamnan Kano Abba Kabir Ga Nasiru Yusuf Gawuna

“A matsayina na, na ɗan asalin jihar Kano, ina ganin wannan ita ce hanya mafi sauƙi da zan nuna masa soyayyar da nake yi a kan nasarar da ya samu a kotun ƙoli  kuma ina fata da kuma addu’ar Allah ya ba shi ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ya fara wa al’ummar Jihar Kano.”

Leave a Reply