No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babban Darakta na Asibitin ƙwararru na jihar Ekiti, Ikere-Ekiti, Dakta Olubiyi Olaolu Abidemi ya yi wa matarsa ​​dukan tsiya sakamakon rashin jituwa da suka samu a gidansu da ke asibitin St. David Compound Ifaki-Ekiti a ranar Alhamis, 14 ga Satumba, 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Likitan ya fusata ne bayan da matarsa ​​ta ƙi kula da wata abokiyarsa (ma’aikaciyarsa) kamar yadda ya umarce ta.Wani ɗan uwan matar ya shaida wa jaridar cewa Likitan ya yi barazanar kashe ta kuma ya kama wuyanta ya yi yunƙurin shaƙe ta a gidansu.

Matarsa mai suna Dakta (Mrs) Olubiyi Adenike, malama a Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti, an bayyana cewa ta samu munanan raunuka a wuyanta kuma an kwantar da ita a sashin haɗurran gaggawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti.

An kuma ruwaito cewa CMD wanda ya ƙi yin magana da manema labarai lokacin da aka tuntuɓe shi, ya yi iƙirarin cewa matarsa ​​tana riya duk da an kai ta asibiti.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...