No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani jirgin ɗaukar marasa lafiya ya yi hatsari

Wani jirgi mai sauƙar ungulu na ɗaukar marasa lafiya ya yi hatsari a lardin Mugla da ke kudu maso yammacin Turkiyya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, kamar yadda gwamnan lardin Idris Akbiyik ya tabbatar.

Matuƙan jirgi mutum biyu da likita ɗaya da wani ma’aikacin lafiya sun rasu a lokacin da jirgin ya faɗa a harabar wani asibiti wanda ke a gundumar Mugla Mentese.

Jami’an kashe gobara da ‘yan sanda da kuma jami’an bayar da agajin gaggawa na Turkiyya sun yi gaggawar isa wurin da lamarin ya faru.

Duk da cewa akwai hazo mai yawa a yankin, amma Akbiyik ya ce har yanzu ba a san dalilin da ya jawo hatsarin ba inda ake ci gana da gudanar da bincike.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

Da yake jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, Akbiyik ya ce babu wata barna a cikin asibitin

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...