Wani jirgi da NNPCL ya ɗauka ya yi hatsari a Fatakwal

0
65

Wani jirgi da NNPCL ya ɗauka ya yi hatsari a Fatakwal

Wani jirgi mai sauƙar ungulu da kamfanin mai na NNPCL ya ɗauki shatarsa a Najeriye ya yi hatsari.

Jirgin ya faɗa ruwan teku da misalin ƙarfe 11:22 na ranar 24 ga watan Oktoba ɗauke da mutum 8 a birnin Fatakwal a jihar Rivers.

“Mun ka sa samun jirgin mai lamba 5NBQG wanda kamfanin NNPCL ya ɗauki shata wanda kuma ya taso daga filin jiragen sama na sojin Najeriya a Fatakwal.

“Jirgin mallakin kamfanin East Winds Aviation ne.” Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Darektan yada labarai Olufemi Soneye.

KU KUMA KARANTA:NNPCL ta musanta zargin MURIC na yi wa matatar man Ɗangote maƙarƙashiya.

A cewar NNPCL, mutum takwas ne a cikin jirgin wadanda suka hada da fasinja 6 da matuka biyu.

“Ya zuwa yanzu an ciro gawarwakin mutum uku” in ji sanarwar.

Jirgin na helikwafta ya fada cikin ruwan Bonny Finima ne da ke hade da Tekun Atilantika kamar yadda hukumomi suka fada.

Bayanai sun yi nuni da cewa ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana can ana gudanar da ayyukan ceto sauran mutanen da ba a gani ba.

Leave a Reply