Wani hedimasta ya yi wa ‘yar shekara shida fyaɗe

An kama wani hedimasta a jihar Bauchi da laifin yi wa ‘yar shekara 6 fyaɗe.

Mai shari’a Nana Fatimah Jibrin, shugabar babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 11, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan kaso ga wani Hedimasta a garin Burra da ke ƙaramar hukumar Ningi mai suna Jalaludeen Zakari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata yarinya yar shekara 6.

Yarinyar ta kasance a makarantar don yin jarabawar shiga makarantar amma Zakari ya tsare ta tsawon sa’o’i bayan an rufe makarantar a hukumance.

Barista Dayabu Ayuba, lauya mai shigar da ƙara kuma lauyan jiha a ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2023, ya ce wanda ake tuhumar ya shigar da yatsarsa a cikin al’aurar yarinyar.

KU KUMA KARANTA: Shekara 3 bayan ya yi wa ‘yar shekara 4 fyaɗe, kotu ta yanke mishi hukunci

Ayuba ya ce a lokacin da ake shari’ar, shaidu uku ciki har da wanda aka yi wa lalata, sun ba da shaida a gaban kotun.

“Mai laifin ya buƙaci yarinyar da ta tsaya, ya sallami sauran ɗaliban bayan an tashi daga makaranta, ba tare da bayar da dalilin tsawaita zaman yarinyar ba. 

Yayin da aka bar ta a baya, hedimasta ya ya kai mata harin lalata, wanda ya yi daidai da fyaɗe a shari’ance,” inji shi.

Ayuba ya ce an yanke hukuncin ne a watan Yulin wannan shekara bayan Jalaludeen ya roƙi kotu da ta yi masa sassauci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *