Connect with us

Hatsari

Wani ɗan sanda a Anambra ya mutu a hatsarin mota

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin jami’anta ASP Anthony Ogbodo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Ikenga Tochukwu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Awka, a ranar Lahadi, ya ce jami’in ya rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da babur ɗinsa da wata motar safa a ranar Asabar, 16 ga Satumba, 2023.

A cewarsa, direban motar bas ɗin da ya kakkaɓo jami’in ya kai shi Asibiti da ke Enugwu Ukwu kafin ya rasu.

“An kama direban kuma an kai shi kurkuku yayin da ake gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.

KU KUMA KARANTA: Mutane 14 sun mutu, sakamakon hatsarin jirgin sama a Brazil

“Wannan shi ne don ƙaryata maganganun ɓatanci da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na alaƙanta mutuwar jami’in da dalilai daban-daban.

“Rundunar ‘yan sandan ta yi alhinin rasuwar jami’in tare da yin ta’aziyya ga iyalansa da masoyansa bisa wannan mummunan rashi da ya yi.

“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Aderemi Adeoye ya ba da tabbacin cewa za a gaggauta yin adalci a shari’ar,” in ji Ikenga.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane biyar a hanyar Legas zuwa Ibadan | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hatsari

Jirgin sojin Najeriya ya faɗo a Kaduna

Published

on

Jirgin sojin Najeriya ya faɗo a Kaduna

Jirgin sojin Najeriya ya faɗo a Kaduna

Wani jirgin sama na sojin Najeriya ya yi hatsari a ƙauyen Tami da ke yankin Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin ya ce jirgin sojin mai sauƙar ungulu ne, kuma ya yi hatsari ne da misalin karfe 5 na asubar Litinin din nan.

Mazauna yankin sun bayyana cewa matukin ya fito daga cikin tarkacen jirgin da ya fado.

Bayan nan sojoji suka yi gaggawar zuwa suka yi wa yankin kawanya tare da fara bincike.

Sojojin sun kuma hana mutane isa wurin da tarkacen jirgin yake.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

An ce jirgin yana tsaka da aikin sintiri a yankin ne ya samu matsala, lamarin da ya haddasa faduwarsa.

Kawo yanzu Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ba ta fitar da sanarwar game da lamarin ba.

Continue Reading

Hatsari

Wani mummunan hatsari yayi sanadiyyar mutuwar mutane 16 daga cikin 18 da ke motar

Published

on

Wata motar fasinja da ta taso daga Bauchi ta yi hatsari a Inugu kuma mutum 16 daga cikin fasinjoji 18 dake motar maza 14 mata 2 sun mųțtu, wasun su ma ba a iya gane su don sun ƙone ƙurmus.

‘Yan sanda sun ce lamarin ya faru da yammacin jiya Talata, 30 ga watan Afrilu a babban titin garin Ekwegbe.

KU KUMA KARANTA: Fasinjoji sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Kogi

Motar ƙirar Toyota Hummer Bus ce 18 seater dauke da lambar Bauchi, DAS 215 XA, kuma an rubuta “Masha Allah” a jikin motar.

Don haka Kwamishinan yan sanda na Enugu ke roƙon jama’a duk wanda Allah yasa ya san wani daga cikin fasinjojin to a tuntubi rundunar a 08098880172 ko 08086671202

Continue Reading

Gobara

Mutane da dama sun mutu, sakamakon fashewar tankar mai a Fatakwal

Published

on

Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a hanyar East-West Road a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a kudancin Najeriya.

Jaridun Punch da na Vanguard sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:45 na daren Juma’a.

Bayanai sun yi nuni da cewa bayan da tankar ta mai ta kama da wuta, ta shafi motoci aƙalla goma da ke jerin cunkoson ababen hawa a birnin na Fatakwal.

KU KUMA KARANTA:Matatar man Fatakwal za ta koma bakin aiki cikin watan Afrilu – Kyari

Wani da ya shaida lamarin ya faɗawa jaridar Vanguard cewa ya ji ƙara har sau biyu masu firgitarwa daga baya kuma hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya.

“Idan kuna da ‘yan’uwa a Fatakwal ku ƙira su don ku ji lafiyarsu” Wani mazaunin birnin na Fatakwal mai suna Bassey Esang Don, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a san musabbabin fashewar da ta auku ba ko iya sanin adadin mutanen da suka mutu.

Faɗuwar tankar mai ta kama da wuta ba baƙon abu ba ne a Najeriya, inda a wasu lokuta mutane kan yi rububin zuwa kwasar man idan yana Malala.

Daga nan ne kuma akan samu akasi har wuta ta kama ta laƙume rayukan mutane.

Wannan al’amari na faruwa ne yayin da farashin mai ya ƙara tsada a Najeriya inda litar mai ta kusa kai wa Naira 1,000 a sassan ƙasar.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like