No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani ɗalibi ɗan shekara 22 a makarantar Sheikh Kamaldeen Arabic da ke Ilorin a jihar Kwara ya kashe kansa.

Ɗalibin mai suna Alfa Musa, an same shi ne a rataye a ɗakinsa da ke harabar Dagbenu a unguwar Ogidi a Ilorin a ranar Alhamis 7 ga watan Disamba, 2023.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ejire Adetoun Adeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an fara bincike kan lamarin.

PPRO ya ce marigayin ya bar wa iyayensa takardar kashe kansa watau “suicide note” .

KU KUMA KARANTA: Ɗan kasuwa ya nemi kashe matarsa don ya ƙara jari a shagonsa

“Mama da baba na, ku yi hakuri, na yi haka ne saboda Allah bai amsa addu’ata ba, gwamma in mutu da in aikata zunubi, don Allah, ku gafarta mini, ina son ku, ku binne ni a gida.”

An tattaro cewa ɗaya daga cikin abokansa ya kai ziyara gidansa a ranar da lamarin ya faru amma ya tarar da ƙofar ɗakinsa a kulle.

Bayan an yi ta ƙwanƙwasa ƙofa ba tare da an ba da amsa ba, sai aka bude kofar da karfi, aka ga marigayin a rataye.

An gan bokitin fenti da babu komai a ciki wanda ake zargin ya kife ya hau ya rataya kansa a ɗakinsa.

Wani makwabcin ya bayyana marigayin wanda ya fito daga jihar Osun a matsayin musulmi mai kishin addini.

A halin da ake ciki, ɗaya daga cikin abokan aikinsa ya saka hoton bidiyo daga sallar jana’izar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...